An yi wata girgizar ƙasa cikin teku a Indonesiya. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wata girgizar ƙasa cikin teku a Indonesiya.

A ƙasar Indonesiya, inda igiyar ruwan nan ta tsunami ta janyo asarar rayukan ɗimbin yawan mutane a kan tsibirin Java, an sake yin wata girgizar ƙasa a ƙarƙashin teku, a tsibirin Sulawesi, abin da ya janyo fargabar aukuwar wata annobar kuma ta tsunami. Wani jami’in kula da yanayin sararin samaniya na ƙasar ya faɗa wa maneman labarai cewa, an gano cibiyar girgizar, wadda ta kai ƙarfin awo 6 da ɗigo 6 a mizanin Richter, a wani wuri ne mai nisan kilomita 90 a kudu maso gabashin birnin Gorontalo.