An yi tattaunawa kan makomar Burkina Faso | Labarai | DW | 02.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi tattaunawa kan makomar Burkina Faso

Sabon shugaban gwamnatin mulkin soji na Burkina Faso Issac Zida yana ganawa da 'yan adawa

Shugaban rikon gwamnatin wucin gadi a kasar Burkina Faso Yacouba Issac Zida ya gana da jagoran yan adawan kasar. Daga cikin wadanda suka hallarci ganawar da aka yi, sun hada da jagoran 'yan adawa a majalisar dokokin kasar, Zephirin Diabre, da tsohon ministan harkokin wajen kasar Ablasse Ouedraogo, kana da tsohon firaministan kasar Roch Marc Christian Kabore, da kuma kakakin jama'ar da ta yi boren da ya kifar da gwamnatin Blaise Compaore, wato Benewende Sankara.

Ganawar dai ta biyo bayan rashin amincewa da mutimin da sojoji suka nada don ya jagoranci gwamnatin wucin gadi, inda talakawan kasar ke cewa dole a bai wa wani farar hula ya jagoranci gwamnati, domin kuwa in suka yarda da wani soja, tamkar an yi musu kwace bayan azabar da suka sha wajen kifar da gwamnati Compaore.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo