Taron inganta shari'a a Jamhuriyar Nijar
May 7, 2026
A Jamhuriyar Nijar babban mai shigar da kara na gwamnati ya yi wani zama da shugabannin jami'an tsaro masu binciken laifuka, a wani mataki na samun cikakar fahimtar juna da kuma zaburar da jami'an tsaron kan batutuwan da suka shafi ayyukansu na bincike tare da mutunta hakkokin jama'a da kyaukyawan tarbo ga wadanda ke zuwa domin gabatar da kara a ofishin yan sanda daban-daban ko na Jandarma, tare da inganta bincike tun daga tushe kafin ma karan yake zuwa a gaban alkali.
Aiki cikin gaskiya
Kaman dai yadda aka riga aka sani batun shari'a na daga cikin mahimman batutuwa guda hudu da shugaban kasar na mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani na jamhuriyar Nijar ya sa wa gaba don ganin al'umma ya iganta ta yadda al'umma za ta yarda da ma'aikatun kasa na shari'a da ma tsarin shari'ana kasar.
Ta sabili da haka ne daga nashi bangare babban mai shigar da kara na gwamnati baya maga fadakarwa da yake yi ta shafukan sada zumunta, ya shirya wata haduwa a ofishin 'yan sanda masu bincike na farin kaya da ake kira PJ domin tattauna batutuwa da ke da babban mahimmanci ga tafiyar shari'a a kasar ta Nijar.
Sau tari dai mutane na korafe-korafe kan mashara'antu ko kuma osfisoshin jami'an tsaro masu bincike, inda wasu lokuttan mutane ke fuskantar tsangwama daga wasu ma'aikatan alhali duk ma'aikaci yana aikin shi ne domin al'umma kuma gudanar da aikinsa yadda ta kamata ne zai taimaka wajen ci-gaban kasarsa.
Binciken jami'an tsaro
To ko yaya su jami'an tsaro masu bincike suka ji da kiran da babban mai shigar da kara ya yi musu na ganin sun kyautata tafiya daga cikin ayyukansu na neman sanin sanin yadda abubuwa suka wakana kafin a tura zuwa ga alkali mai shari'a? Kwamishina Issoufou Harouna Ali, babban darektan ma'aikatar 'yan sanda masu bincike ta PJ ya ce irin wannan zama yana da babban mahimmanci a gare su saboda batun kare hakkin jama'a kamarf yadda doka ta tanada.
Abin jira a gani dai shi ne sauyi da al'umma za ta gani nan gaba a wuraren shigar da kara na jami'an tsaro masu bincike tun ma daga batun yadda ake tarbon mutun da kuma sauraronsa cikin tsanaki don ganin masu zuwa wajen hukuma na samun cikakar nutsuwa ta bayyana gaskiyar lamari ba tare da sun yi wasa da shari'a ta hanyar boye gaskiya ba.