An yi korafi kan yadda ake kidayar kuri´u a Kongo | Labarai | DW | 05.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi korafi kan yadda ake kidayar kuri´u a Kongo

Ana kara yin suka ga yadda ake kidayar kuri´u na zaben gama gari na farko cikin shekaru fiye da 40 da aka gudanar a kasar JDK ranar lahadi da ta gabata. Tun a ranar laraba da ta gabata masu sa ido na kasa da kasa sun yi korafin cewa ba´a yi wani shiri mai gamsarwa ba a dukkan wurare 62 na tattara kuri´u dake fadin kasar. Wani wakilin MDD da ya ki a ambaci sunan sa ya ce ana cikin hali na rudami a dukkan wuraren. Yace hakan zai ba wa al´umar wata damar yin zargin tabka magudin zabe. Anneke Van Woudenberg ta kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Watch wadda a halin yanzu take lardin Ituri ta bayyana zargin da ake yi na aringizon kuri´un tana mai cewa.

“Ni da kai na na ga an zubar da kuri´u masu yawan gaske a wajen ofisoshin. Ba wanda ya kirga wadannan kuri´u kuma ba wanda zai iya tabbatar da sahihancin su. Wai shin hakan na nufin ke nan an yi magudi? Zai yi wuya a fadi haka a yanzu. To amma hakika ana gudanar da wasu abubuwa da ba su dace ba.”