An yi kira ga hukumomin Myanmar da su nuna dattako | Labarai | DW | 24.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga hukumomin Myanmar da su nuna dattako

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya yaba da zanga-zangar lumana da ake yi a Myanmar sannan a lokaci daya yayi kira ga gwamnatin mulkin sojin kasar da ta nuna halin ya kamata. Mai magana da yawon Ban Michele Montas ta ce babban sakataren na MDD ya yaba da matakin da masu zanga-zanga ke dauka gabatar da bukatunsu cikin ruwan sanyi. Ita ma KTT ta yi kira ga gwamnatin mulkin sojin da ta sasanta da masu zanga-zangar. Kakakin babban jami´in diplomasiyar kungiyar EU Javier Solana, ta ce mista Solana ya nemi hukumomin kasar da su saki firsinonin siyasa sannan su fara aiwatar da canje canje. A yau dai sama da mutane dubu 100 suka yi cincirindo a manyan titunan birnin Rangoon, inda suka hadu da ´yan addinin Bhudda wadanda ke bijirewa gwamnati.