An yi kira ga EU da ta saka Masar a kokarin magance kwararar bakin haure | Labarai | DW | 20.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga EU da ta saka Masar a kokarin magance kwararar bakin haure

Gwamnatin kasar Ostiriya ta yi kira ga sauran kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da su gayyayto kasar Masar cikin batun kawo karshen kwararrar 'yan cirani kasashen Turai daga nahiyar Afrika.

Shugaban gwamnatin Ostiriya Sebastian Kurz wanda a halin yanzu yake rike da mukamin shugabancin Kungiyar Tarayyar Turai tare da Shugaban hukumar zartarwar kungiyar, Donald Tusk, sun kai wata ziyarar aiki kasar Masar cikin makon da ya gabata, inda kuma suka tattatuna da shugaban kasar Abdel-Fattah el-Sissi kan batun na 'yan cirani tare kuma da yaba masa kan matakin da ya dauka na hana ketara wa Turan ta hanyoyin ruwan kasar Masar.

Kasashen Kungiyar Tarayyar Turan dai na gudanar wa wani taron koli a birnin Salzburg na kasar ta Ostiriya, inda batun 'yan cirani ke a cikin jadawalin da shugabannin suka tattauna kai.