An yi kira da a sake komawa ga tura taimako ga Falasdinawa | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a sake komawa ga tura taimako ga Falasdinawa

´Yar takarar shugaban kasar Faransa karkashin tutar jam´iyar ´yan Socialist Segolene Royal ta yi kira ga kasashe duniya da su sake komawa da kai dauki ga Falasdinawa. Yayin ziyarar da ta kai Zirin Gaza a yau lahadi Madame Royal ta ce al´umar Falasdinu na matukar bukatar taimako musamman wajen farfado da ayyukan hukuma. Royal dai na muradin zama mace ta farko da zata dare kan kujerar shugabancin Faransa, inda zata yi takara da ministan harkokin cikin gida Nicolas Sarkozy ma zaben shugaban kasar da zai gudana a ranar 22 ga watan afrilun shekara mai zuwa. Bayan nasarar da kungiyar Hamas ta samu kasashen duniya sun katse tura duk wani taimako ga Falasdinawa saboda kungiyar ta masu kishin islama ta ki amincewa da Isra´ila.