An yi kira da a kula da kyautata ilimin mata | Labarai | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a kula da kyautata ilimin mata

Michelle Obama ce ta yi wannan kira ga takwarorinta na Afirka da su kula da ilimin mata, bayan taron kolin da ya gudana tsakanin Amirka da kasashwen Afirka.

Uwargidan shugaban Amirka Michelle Obama, a wannan Larabar ta yi kira ga takwarorinta matan shugabannin kasashen Afirka, da su bada himma na ganin kananan yara 'yan mata sun samu ilimi a kasashensu. Michelle Obama ta yi wannan kira ne a rana ta karshe na babban taron kasashen Afirka da Amirka da ke gudana a birnin Washington. Ta kuma yi kira ga bada goyon baya ga 'yan matan nan da 'yan Boko Haram suka sace a garin Chibock na jihar Borno a Najeriya inda ta kara da cewa bai kamata a ce wata mace na tsoron zuwa makaranta ba.

Wannan babban zaman taron tsakanin Afirka da Amirka, ya samu halartar akalla shugabannin kasashe da na gwamnati 40 daga Afirka, inda suka dukufa kan batun bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen da kuma makomar mata a Afirka.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal