An yi kira da a ƙara yaqwan dakarun zaman lafiya a Afghanistan | Labarai | DW | 11.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a ƙara yaqwan dakarun zaman lafiya a Afghanistan

Kwamnadan dakarun kasa da kasa a Afghanistan Manjo janar Bruno Kasdorf ya yi kira da a tura musu karin sojoji. Ya fadawa kamfanin dillancin Jamus DPA cewa sojoji dubu 40 dake karkashin sa a halin yanzu ba zasu iya tabbatar da tsaro a fadin kasar baki daya ba. hakan kuwa yana da muhimmanci wajen sake gina Afghanistan. To amma janar din wanda Bajamushe ne bai fadi yawan sojojin da yake bukata ba. yayi kira ga kasarsa da ta ci-gaba da ba da gudunmawa a ayyukan tabbatar da zaman lafiya da kuma sake gina Afghanistan. A cikin wata mai zuwa majalisar dokokin Jamus zata kada kuri´a a dangane da kara wa´adin aikin sojin ta Afghanistan. A jiya an kashe mutane kusan 30 sannan wasu 60 suka jikata a wani hari kunar bakin wake da aka kai a lardin Helmand dake kudancin Afghanistan.