An yi hatsarin jirgin kasa a Masar | Labarai | DW | 11.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi hatsarin jirgin kasa a Masar

Mutane 36 suka rasa rayukansu a arewacin Masar bayan da wasu jiragen kasar guda biyu suka ci karo da juna kusan da birnin Alexandria.

Kafofin watsa labarai na Masar sun ce hadarin ya faru ne a lokacin da daya daga cikin jiragen, ya tsaya kan hanya bayan ya samu wata yar guntuwar matsala. Jiragen biyu wadanda daya ya taso daga birni Alkahira zuwa Alexandria, kana daya ya fito daga Port Said a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alexandria sun ci karo a cikin jeji.