1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yankewa Musharraf hukuncin kisa

Abdoulaye Mamane Amadou
December 17, 2019

Wata kotu a Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga tsohon shugaban kasar Pervez Musharraf bisa tuhumarsa da aikata laifin cin amanar kasa da yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/3UwLB
Ehemaliger pakistanischer Präsident Pervez Muscharraf
Hoto: picture-alliance/AP

Wani kusa a gwamnatin kasar ta Pakistan da ya tabbatar da wannan hukuncin da ta yi kan Musharaf din ya ce tsohon shugaban ya aikata laifin da ya kai ga yanke masa hukuncin kisa ne bayan ya taka doka mai lamba shida ta kundin tsarin mulkin kasar.

A shekarar 2007 shugaban kasar ya ayyana dokar tabaci a kasar lamarin da aka zarga da cewa aikata laifin cin amanar kasa ne.