An watse baran baran a taron yankin palasdinawa | Labarai | DW | 20.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An watse baran baran a taron yankin palasdinawa

Bangarori masu adawa da juna na yankin palasdinawa sun dakatar da tattaunawarsu dangane da kafa gwamnatin hadin kann yankin ,sakamakon rashin cimma daidaito kann mukaman ministoci.An bayyana cewa Shugaba Mahmoud Abbas na kungiyar Fatah,ya fice daga cikin zauren tattaunawar daya gudana a Gaza cikin bacin rai,bayan prime minister Ismail Haniyeh ya nemi,kungiyarsa ta hamas mai mulki tacigaba da rike mukaman ministocin harkokin kudi dana cikin gida.A yan watanniya da suka gabata dai,shugaba Abbas da Premier Haniyeh sunyi kokarin kafa gwamnatin hadaka a yankin Palasdinu,domin ceto kasar daga takunkumin tallafi da kasashe sukayi wa gwamnatin na hamas.