1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ware kwanakin makoki a Muzambik

March 20, 2019

Hukumomi a Muzambik sun ware kwanaki uku na zaman makokin asarar rayuka da kasar ta gani sakamakon mahaukaciyar guguwar nan ta ta shafi kasa.

https://p.dw.com/p/3FN8R
Mosambik Unwetter Zyklon Idai
Hoto: Getty Images/AFP/A. Barbier

Bayanai sun ce hanyoyin sadarwa sun sake dawowa a birnin Beira na kasar ta Muzambik, wanda ya fi fuskantar barnar da mahaukaciyar guguwa ta haddasaa 'yan kwanakin nan.

Kamfanin wayoyin sadarwa a kasar ya tabbatar da dawowar hanyoyin a wata sanarwar da ya wallafa ta shafukan sada zumunta.

Birnin na Beira dai na dauke ne da mutum akalla dubu 500, kuma a halin da ake mazauna yankunan da bala'in ya shafa na fama da tsananci kunci ne da kuma juyayi. 

Sun kuma yi kiyasin akalla an rasa sama da mutum 200, kuma a farkon wannan makon ne Shugaba Filipe Nyusi na kasar, ya ce mutuwa ka iya shafar sama da mutum dubu guda.