An umarci masu zanga-zanga da su bar fadar shugaban Masar
December 6, 2012Talla
Gabannin wannan sanawar dai jagoran jami'iyyar 'yan uwa Musulmi ta shugaba Mursi ya yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin tashin hankali ba zai haifawa kasar da mai idanu ba yayin da kasahsen Burtaniya da Amurka su ka nuna damuwarsu dangane da tada kayar bayan inda su ka shawarce su da sasanta.
Nan gaba ne dai a yau ake sa ran Shugaba Mursi zai yi jawabi ga al'ummar kasar sai dai fadar shugaban kasar ba ta tantance kan abubuwan da jawabin na shugaban zai maida hankali a kai ba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal