An tuhumi Oscar Pistorius da zargin kisa | Labarai | DW | 19.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuhumi Oscar Pistorius da zargin kisa

Kotu ta tuhimi dan tseren nan na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius da zargin hallaka budurwarsa bayan da ya gurfana gaban alkali inda aka ware watan Maris din 2014 don fara shari'a.

Oscar Pistorius enters the dock before in court proceedings at the Pretoria Magistrates court June 4, 2013. Blade Runner Pistorius arrived at court on Tuesday in his first formal appearance since his release on bail in February for the Valentine's Day killing of his girlfriend, 30-year-old model Reeva Steenkamp. REUTERS/Mike Hutchings (SOUTH AFRICA - Tags: CRIME LAW SPORT)

Oscar Pistorius Anhörung

A wannan Litinin din ce dan tseren nan na Afrika ta Kudu Oscar Pistorius ya gurfana a gaban wata kotun majistre inda kotun ta tuhume shi da zargin hallaka budurwarsa Reeva Steenkamp a cikin watannin da su ka gabata.

Pitorius dan shekaru 26 da haihuwa ya bayyana ne a kotun tare da 'yan uwansa rike da hannun juna, inda ya yi ta share hawaye gabannin fara zaman kotun.

Zaman kotun na yau da ma dai wannan tuhuma da aka yi masa na zaman damba ta fara shari'ar da za yi masa bayan da masu gabatar da kara su ka gabatarwa kotu takardun kara da kuma jerin sunayen shaidu da yawansu ya kai dari.

A ranar uku ga watan Maris na badi ne dai za a fara shari'ar gadan-gadan a wata babbar kotu da ke birnin Pretoria inda zai iya fuskantar daurin rai da rai to sai dai gabannin tuhumar tasa, Pistorius ya ce ya harbe budurwar tasa ce bisa kusukure domin ya yi zaton wani ne ya kutso masa kai cikin gida, yayin da masu gabatar da kara su ka ce ya kashe ta ne da saninsa bayan da su ka yi fada.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal