An tsige shugabar kasar Brazil | Labarai | DW | 31.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsige shugabar kasar Brazil

Michel Temer ne zai maye gurbin Dilma Rouseff a mastayin shugabancin rikon kwarya, to sai dai Dilma ta samu afuwar rabata da aiyukan gwamnati.

'Yan majalisan kasar Brazil sun kada kuri'a da ya kai ga sauke Shugabar Dilma Rouseff daga kan karagar mulkin kasar, adadin sanatoci 61 ne dai suka kada kuri'ar amincewa da shugabar ta saba kundin tsarin mulki na yin katsalandan a kasafin kudi da ya jawo mata zargin almundahana da neman yin tazarce.

To sai dai a wani zabe na daban da aka yi mai cike da zazzafar mahawara na takawa Dilma birki a dukkanin lamuran da ya shafi harkokin siyasa da ma gwamnati a kasar har na tsawon shekaru tawakas bai yi tasiri ba.

A yanzu dai Michel Temer mai shekaru 71 ne zai maye gurbin shugaba Dilma a matsayin rikon kwarya. Tuni dai magoya bayan tsohuwar shugabar ke bayyana fargar tsige Dilma zai jefa kasar cikin rikicin siyasa.