An tsayar da ranar zaben Laberiya | Labarai | DW | 12.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsayar da ranar zaben Laberiya

A wannan Talata hukumar zaben kasar Laberiya ta sanar da tsayar da ranar ashirin da shida ga wannan watan na Disamba a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na biyu na babban zaben shugabancin kasar.

Shugaban hukumar zaben Jerome Korkoya ne ya fadi hakan a dazu dazun nan.Ya kuma ce za a kawo karshen duk wani kamfain a ranar ashirin da hudu. Za a fafata ne a tsakanin tsohon gwarzon wasan kwallon kafa na duniya George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai, an jinkirta zaben kasar ta Laberiya, bayan da dan takara Charles Brumskine na jam'iyyar adawa ta Liberty da ya zo na uku a fafatawar farko ya yi zargin cewa an tafka magudi, a makon da ya gabata kotu ta yi watsi da karar dan takarar kan zaben.