An tsayar da lokacin gudanar da zaɓe a Kodivuwa | Siyasa | DW | 06.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An tsayar da lokacin gudanar da zaɓe a Kodivuwa

Ɓangarorin da ke gaba da juna a Kodivuwa sun amince da ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar zaɓe a ƙasar

default

Shugaban Kodivuwa Laurent Gbagbo

Hukumomin a ƙasar Kodivuwar sun yi amfani da tarurrukan share fagen gudanar da bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga Faransa wajen tsayar da ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa. Ɓangarorin da ke gaba da juna a ƙasar dai sun amince da ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar zaɓe da zai baiwa ƙasar damar kawo dambarwar siyasa.

Birinin Yamoussoukoro da ke zama mahaifar marigayi Houphouet Boigny da ya samowa ƙasar Kodivuwar 'yancin kai daga Turawan Faransa, gwamnatin wannan ƙasa ta yi amfani wajen bayyana ranar cewa cikin ranuka 84 ne 'yan ƙasar za su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen sabon shugaban ƙasa. Wannan mataki mai matikar mahimmaci ga Kodivuwar da masu faɗa a jinta suka shafe shekaru suna kai ruwa rana tsakaninsu, zai zo watanni biyu bayan bikin kewayowar ranar samun 'yancin kai da ke gudana a wannan Asabar. Lamarin da Oceane Bamba, malamar kimiyar siyasa a jami' ar Abidjan, ta ce idan aka duba da idon basiri, bai kamata a gudanar da bikin ranar 'yancin ba.

"A fuskar tattalin arziki, bashi yayi mana katutu. A fuskar tsaro Kodivuwa ba ta da iko sayan makami ko da guda ne. Yayin da a fuskar diplomasiya, ba mu da 'yancin yin gaban kanmu ba tare da amincewar masu shiga tsakani daga waje ba. Ayar tambaya a nan ita ce, wai shin mai yayi mana daɗi, da har zai kai mu ga gudanar da bikin samun 'yancin kai."

Sai dai hukumomin na son amfani da wannan dama wajen nuna irin fahimtar juna da aka samu tsakanin ɓangarorin da suka shafe shekaru ba sa ga maciji da juna, musamman ma tsakanin firaminista mai ci a yanzu wato Guillaume Soro da kuma shugaba Laurent Gbagbo. Da kuma tsakanin tsohon firaminista Alhassan Ouatara da a baya aka haramta masa tsayawa takara da kuma ɓangaren da ke mulki. Lamarin da a cewar hukumomin Abidjan alama ce da ta ke nuna cewa shugabanninta a shirye suke su rungumi duk sakamakon da zaɓen zai haifar. Sai dai inda gizo ke saƙa a cewar wani ɗan kasuwa mai suna Prospere Nguessan, shi ne ɗage zaɓen da aka yi ta yi, ya saɓawa alƙiblar da aka ɗora ƙasar akai.

"Gadon da wanda yayi gwagwarmayar ƙwato mana 'yanci ya bar mana ba a alkintashi ba. Kuma duk shugabannin da muka samu daga baya, ba su tsinana komai ba."

Dukkanin 'yan takara da ake ji cewa za su iya yin tasiri a zaɓen na 31 ga watan Oktoba a Kodivuwar, sun fara alƙawarin mayar da tattalin arzikin ƙasar kan turba madaidaiciya. Sai dai Charles Sicka, shugaban wata ƙungiya mai zaman kanta a birnin Abidjan, da kamar wuya.

"Ƙarfin tattalin arzikimu a shekarun 1960 yana tafiya kafaɗa da kafaɗa da na Koriya Ta Kudu. Amma a yanzu Koriyar ta tashi daga rukunin ƙasashe 'yan Rabbana ka wadatamu i zuwa ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki. Kodivuwa kuwa ta tashi daga rukunin ƙasashe masu tasowa i zuwa wacce bashi yayi mata katutu."

Batun tantance waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri' a ƙasar ne ke ci gaba da zama zakaran gwajin dafi na yunƙurin gudanar da zaɓen da zai samu karɓuwa ga kowa da kowa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal