An tsare Jirgin makare da makamai a Kano | Labarai | DW | 06.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare Jirgin makare da makamai a Kano

Wani jirgin sama da ya taso daga Bangui zuwa Chadi makare da makamai da jirage uku masu saukar angulu a cikinsa ya fada hannun jami'an tsaro a tashar jiragen Malam Aminu Kano

Il-86

Jirgin da ke dauke da makaman harba roka da sauransu, an tsare shi ne a tashar jeragen sama na Malam Aminu Kano. Jigrin saman dai ya ta so ne daga birnin Bangui Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, kuma zai wuce kasar Chadi ne kafin a kama shi makare da makamai, kana a cikin jirgin akwai wasu jiragen Helikwapta, wato masu tashin angulu 3. Yanzu haka dai ko wa na iya zuwa tashar, kuma zai ga jirgin, inda mataimakin gwannan Kano Dr Ganduje da kansa aka ce ya nufi tashar jirgin, don gane wa idanunsa. Babu tabbas inda aka nufa da makaman ko kuma wanda ya shigo da su, amma ana kyautata zaton makaman na alaka da kungiyar Boko Haram wanda ta addabi arewacin Najeriya.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango.
Edita: Usman Shehu Usman