An tsananta tsaro a New Zealand
March 18, 2019Talla
Wani mai suna Brenton Tarrant ne ya kai harin kan musulmi a masallatai biyu daban-daban inda ya halaka mutane 50 wasu kusan adadin ma suka jikkata.
Firaministar kasar, Jacinda Ardern, ta ce za a fidda sabbin dokoki kan mallakar bindiga cikin kwanaki goma.
Tuni kuwa aka garkame maharin yayin da ake ci gaba da bincike cikin wasu kasashen, kuma gwamnatin kasar na shirin wani zama na majalisar ministoci kan sabbin matakan tsaro.
Da ranar wannan Litinin ne ake sa ran gudanar da jana'izar wasu daga cikin wadanda lamarin na Juma'ar makon na jiya ya rutsa da su.