1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma bincike kan kamfanin Boeing

March 19, 2019

Kamfanin kera jiragen nan na Boeing da ma hukumomin da ke sa ido kan jirage a Amirka na ci gaba da fuskantar matsi da bincike a kan yanda aka yi suka amince da ingancin jirage kirar 737 Max 8.

https://p.dw.com/p/3FHXh
Boeing 737 MAX 8
Hoto: Getty Images/J. Raedle

Tsananta binciken ya samo asali ne daga kamanceceniyar da aka samu daga bayanan hadarin jiragen kamfanonin Lion Air na kasar Indonesiya a bara da kuma na kamfanin Ethiopian Airlines a 'yan kwanakin nan inda mutum 157 suka salwanta.

Jim kadan bayan faduwar jirgin na Ethiopian Airlines, babban alkalin birnin Washington na Amirka ya gayyato mutum na farko da ke da hannun wajen bayar da izinin amfani da jirgin wanda sabo ne a jerin jiragen da kamfanin Boeing ya kera a baya-bayan nan.

Ba kasafai ba ne dai hukumomin Amirka ke amince wa bincike kan hadarin jiragen ba, idan aka danganta da yadda kasar Faransa ke yi.