An soke bikin ranar ′yanci a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 08.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soke bikin ranar 'yanci a Sudan ta Kudu

Fadar gwamnatin Sudan ta Kudu ta rude da karar harbe-harben bindigogi, wannan rudani ya yi sanadiyyar soke shirin bukukuwan 'yancin kai da kasar ke shirin gudanarwa a ranar Asabar.

Südsudan Juba Inaugurierung Rebellenführer Riek Machar

Riedk Machar a hagu da Salva Kiir a dama

A wannan Jumma'a fadar gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da ke birnin Juba ta rude da karar harbe-harben bindigogi, wanda kuma ya yi sanadiyyar soke shirin bukukuwan 'yancin kai da kasar ke shirin gudanarwa a wannan Asabar. Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar ke ganawa da manema labaru.

An dai dauki lokaci mai tsawon ana jin karar harbe-harben bindigogi mai karar gaske a babban birnin kasar Juba. To sai dai babu wani karin bayani da shugabannin biyu suka yi bayan lafawar harbe-harben. A karon farko ne dai dakarun kasar suka yi karambatta da 'yan tawaye wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Salva Kiir biyar tun bayan da dukkanin bangarorin suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Augustan shekara ta 2015.