1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kyamar baki a Afirka ta Kudu

Zulaiha Abubakar MNA
April 15, 2019

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta bukaci gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta gurfanar da wadanda ke da hannu a rikicin kyamar bakin da ya rutsa da mutane 300 'yan asalin kasar Malawi.

https://p.dw.com/p/3GnMO
Südafrika fremdenfeindliche Angriffe auf Migranten
Hoto: AFP/R. Jantilal

A ranar 25 zuwa 27 na watan Maris din da ya gaba ne gungun wasu 'yan sara suka dauke da makamai suka kutsa gidajen 'yan kasashen waje da ke zaune a gabashin kasar ta Afirka ta Kudu suka kore su tare da yin awon gaba da dukiyoyinsu.

Da yake tsokaci game da wannan ta'annati babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar baki na zaman fargaba a Afirka ta Kudu sakamakon yadda marasa aikin yi a kasar ke zarginsu da yin kakagida a ma'aikatu.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta yi Allah wadai da yadda shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya dora alhakin matsalolin da kasar ke fuskanta kan bakin da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba, yayin da yake wani jawabi a taron gangamin jam'iyya. Kasar dai na dauke da miliyoyin baki daga kasashen Afirka.