An sha arangama a Kataloniya | Labarai | DW | 01.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sha arangama a Kataloniya

'Yan sanda a Kataloniya sun yi amfani da kulake da barkono tsohuwa da kuma harsashai na roba wajen tartwatsa dafifin jama'ar da suka fito domin kada kuri'a a zaben raba gardma na amincewa da yancin gashin kai na yanki.

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Kataloniya Carles Puigdemont ya ce abin takaici ne abin da  jami'an tsaro suka yi a kan masu zaben. Ya ce: ''Amfani da karfin da ya wuce kima da gwamnatin Spain ta yi, ba zai hanna al'ummar Kataloniya ba yin zabe cikin ruwan sanhi don demokaradiyya ta tabbata. Kawo yanzu dai mutane  38 suka  jikkata a taho mu gaman, yayin da jami'an tsaro 11  suka samu raunika.