An sanyawa kungiyar Houthi takunkumi | Labarai | DW | 14.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanyawa kungiyar Houthi takunkumi

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da sanya takunkumi musamman ma na makamai kan kungiyar ta Houthi mabiya tafarkin shi'a da ke kasar Yemen wadda ke so karbe iko da kasar.

A dazu ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kakaba wannan takunkumi inda aka amince da shi da kuri'u 14, ko da dai Rasha ta yi rowar kuri'arta bisa dalilinta na son ganon takunkumin ya shafi bangarorin biyu da ke gaba da juna a kasar.

Wannan takunkumi dai zai shafi shugaban kungiyar Abdul-Malik al-Houthi da makarrabansa da suka hada da Abdullah Yahya al Hakim da Abd al-Khaliq al-Huthi da kuma tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh da dansa.