1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar harkokin kasashen wajen Ruwanda ta samu mukami

Zulaiha Abubakar
October 12, 2018

An sanar da ministan harkokin kasashen wajen Ruwanda Louise Mushikiwabo a matsayin babban magatakardan kungiyar Kasashe rainon Faransan yayin babban taron kungiyar a kasar Armeniya.

https://p.dw.com/p/36SqV
München Louise Mushikiwabo Außenministerin Ruanda
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Hase

Jim kadan bayan samun wannan matsayi Mushikiwabo ta jaddada aniyar ta ta ba harshen Faransanci fifiko saboda yadda yaren ya bazu a fadin Duniya,a baya dai kasar Ruwanda ta dora alhakin rikicin kabilancin da ya faru a kasar a shekara ta 1994 kan kasar Faransa lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu. Tuni dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya taya sabuwar babbar magatakardar Kungiyar kasashe Rainon Faransan murna.