An samu mutum na biyu me Ebola a Texas | Labarai | DW | 12.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu mutum na biyu me Ebola a Texas

Jami'ar lafiya a asibitin Texas da suka duba mai cutar Ebola, alamu na nuna cewa ta harbu da kwayoyin cutar kamar yadda gwajin farko na cutar ya nunar .

A jawabin da ya fitar, sashin kula da lafiyar na Texas ta adireshinsa na intanet, ya bayyana cewa za'a sami cikakken sakamako bayan kammala gwaji da cibiyar da ke da alhakin kariya da lura da bazuwar cututtuka ta Atlanta CDC ta fitar.

Dr. David Lakey, da ke zama kwamishinan sashin kula da lafiyar na Texas, ya bayyana cewa suna aiki kafada da kafada da kwararrun na Dallas dan kaucewa ci gaba da bazuwar wannan cuta ta Ebola.

Har ila yau maaikatan na ganawa da mara lafiyar dan gano mutanan da suka yi muamula. Thomas Eric Duncan dai da ya zo da cutar daga Laberiya ya kasance na farko da aka fara gano yana dauke kwayar wannan cuta ta Ebola a kasar ta Amurka wanda kuma ya rasu ta sanadin cutar a ranar Laraba a Dallas.