1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu kulob kulob 4 na Italiya da laifin yin murdiyar wasa

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqW

Manyan kungiyoyin kwallon kafa guda 3 dake rukuni na daya na wasannin lig-lig a Italiya da wata kotu ta same su da laifin yin murdiyar wasanni sun ce zasu daukaka kara don kalubalantar wannan hukunci. A jiya kotun ta birnin Rom ta yanke hukuncin ragewa kungiyoyin Juventus Turin da Lazio Rom da kuma AC Florence daraja inda a badi zasu yi wasannin lig lig a rukuni na biyu maimakon na daya. Hakazalika kotun ta tubewa Club din Juventus kambunta na zama zakara har guda biyu. Kulob din AC Milan wadda ita ma aka same da hannu a wannan abin kunya an cita tara ragewa mata maki 15 to amma zata ci-gaba da wasa a rukuni na daya. An kuma haramtawa dukkan kungiyoyin shiga wasanni a nahiyar Turai a kakar wasa mai zuwa. Tuni dai magoya bayan kungiyoyin suka fara zanga-zangar nuna adawa da hukuncin kotun.