1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaItaliya

An samu ibtila'in dutse mai aman wuta a Italiya

August 16, 2024

Hukumomi a Italiya, sun tabbatar da samun ibtila'in aman wuta daga wani tsauni da ya haddasa turnukewar hayaki da gas mai hadari a sararin samaniyar birnin Sicily.

https://p.dw.com/p/4jXGy
Wata majami'a da ke kusa da tsaunin Etna da ke arewacin Italiya
Wata majami'a da ke kusa da tsaunin Etna da ke arewacin ItaliyaHoto: Salvatore Allegra/AP Photo/picture alliance

An ba da labarin samun ibtila'in dutse mai aman wuta a Italiya. Aman wutar da dutsen Etna ya yi, ya kai ga dakatar da harkokin zirga-zirga a babban filin jiragen sama na Catania da ke a birnin Sicily.

Hukumomin tashar jiragen na Sicily, sun ce tokar da ke saukowa daga dutsen da ke aman wutar ta hana damar jirage su yi amfani da hanyoyinsu na tashi da kuma sauka.

Miliyoyin fasinjoji ne dai ke bi ta tashar ta Catania a duk shekara, sannan kuma wata mahada ce ta masu yawon shakatawa.

Masu aiko da rahotanni sun ce gidaje da tituna ma duk sun kasance cikin duhu, sakamakon yadda toka ke saukowa daga tsaunin na Etna, inda aman wutar ke faruwa.