An samu ɓullar cutar Ebola a ƙasar Mali | Labarai | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu ɓullar cutar Ebola a ƙasar Mali

Aƙalla mutane 43 likitoci ke kulawa da su a ƙasar Mali, bayan da aka gano wata ƙaramar yarinya ɗauke da ƙwayar cutar Ebola.

A jiya Alhamis ne (23.10.2014) ofishin Ministan kiwon lafiyar ƙasar ta Mali ya sanar da samun mutun na farko mai ɗauke da cutar Ebola a wannan ƙasa wadda take wata yarinya ce 'yar shekaru biyu da haihuwa da ta fito daga ƙasar Gini tare da kakarta, wanda sakamakon hakan, aka sanya dukkannin mutanen da ake ganin sun yi mu'amula da ita a ƙarƙashin kulawar likitoci. Daga cikin mutanen 43, akwai jami'an kiwon lafiya guda goma da suka kusanci yarinyar lokacin da aka kai ta wani asibitin yara.

Hukumar lafiya ta duniya WHO da ta tabbatar da wannan labarin a wannan Jumma'ar, ta ce ta aike da ƙwararru zuwa ƙasar ta Mali domin taimaka wa kumomin lafiyar wannan ƙasa don shawo kan wannan matsala. Ƙasar ta Mali dai na matsayin ta shidda a Afirka da aka samu Ɓullar cutar ta Ebola da a halin yanzu tayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 4.900.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane