An sami sauki a hukuncin kisa | Labarai | DW | 11.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami sauki a hukuncin kisa

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International, ta ce an sami matukar raguwar yawan wadanda aka yankewa hukuncin kisa a shekara ta 2016.

Wani sabon rahoton da kungiyar ta Amnesty International ta fitar, na nunin cewa an sami raguwa kan hukuncin kisa a Amirka da ma sauran kasashen duniya. Yanzu dai a cewar rahoton Amirkar ta fita daga jerin kasashe 5 da suka fi yawan daukar matakin kisa kan jama'a.

Haka ma batun yake a kasashen Iran da Pakistan da ke yawan gudanar da hukuncin. Akwai ma wasu kasashen Afirka kudu da hamadar sahara da suma rahoton ya ce an sami wannan sauki.

Amnesty ta ce mutane dubu daya da talatin da biyu aka yankewa hukuncin kisa a duniya, abin da ke zama wani sauki na kashi 37 cikin dari cikin shekaru biyu da suka gabata.