1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami bullar cutar Ebola a Kongo

Ramatu Garba Baba
May 9, 2018

Ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ta tabbatar da labarin bullar cutar Ebola a wani gari da ke a yankin arewa maso yammancin kasar, bayan gwajin jinin da aka yi a kan wasu mutane biyu.

https://p.dw.com/p/2xPEu
Kongo Ausbruch von Ebola
Hoto: Getty Images/AFP/D. Minkoh

Wannan na zuwa ne bayan da jami'an kiwon lafiya a yankin suka soma baiyana fargaba kan wasu mutane ashirin da biyu da suka nuna alamun cutar, akwai wasu goma sha bakwai da suka riga suka mutu da ake zaton a sanadiyar cutar ce.Tuni aka dauki matakin dakile cutar. Yanzu haka ma dai an tura kwararru yankin don sa ido da kuma hana bazuwar cutar da ke saurin halaka dan adam. Rahotannin na cewa wannan shi ne karo na tara da cutar ta Ebola ke bulla a jamhuriyar Kongon.