1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Brazil ya samu sauki

Suleiman Babayo AH
January 5, 2022

Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil ya tabbatar da cewar an sallame shi daga asibiti sakamakon saukin da ya samu daga jinyar cutar hanji da aka yi masa.

https://p.dw.com/p/45Ans
Brasiliens Präsident Bolsonaro liegt in einem Krankenhaus in Sao Paulo
Hoto: @jairbolsonaro/Twitter/REUTERS

A wannan Laraba Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil ya ce an sallame shi daga asibiti bayan da aka yi masa jinya kan cutar da ta same shi a hanji. Tun lokacin yakin neman zaben shekara ta 2018 aka soke shi da wuka yayin gangamin yakin neman zabe.

Dan shekaru 66 da haihuwa shugaban ya bayyana sallamar daga asibiti a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na zamani, tare da wallafa hotonsa da na likitocin da suke kewaye da shi a wani asibitin birnin Sao Paulo na kasar ta Brazil.