An sallami Nelson Mandela daga asibiti | Labarai | DW | 27.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami Nelson Mandela daga asibiti

Hukumomin Afrika ta Kudu sun ce an sallami tsohon shugaban kasar Nelson Mandela daga Asibiti bayan da ya shafe kusan makonni uku a gadon na asibiti ya na jinya.

FILE - This Feb. 29, 2008 file photo shows French President Nicolas Sarkozy, not seen, and his new wife Carla Bruni posing with former South Africa President Nelson Mandela during their visit of the Mandela Foundation in Johannesburg, South Africa. Sarkozy is on a two-day official visit in South Africa. French President Nicolas Sarkozy announced Wednesday that he will seek a second term despite years of low popularity ratings, pledging to boost its lagging economy and protect France's way of life. (Foto:Remy de la Mauviniere, File/AP/dapd)

Symbolbild Nelson Mandela

Nelson Mandela dai ya yi fama ne da cutar huhu gami kuma da tiyata da aka yi masa ta cire duwatsun matsarmama.

Mahukuntan Afrika ta Kudun sun ce jami'an kiwon lafiya za su cigaba da kula da lafiyar Mr. Mandela dan shekaru casa'in da hudu a gidansa da ke birnin Johanesburg har ya samu ya murmure sosai.

Nelson Mandela dai wanda ke zaman shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko ya shafe kimanin shekaru biyu baya fita bainar jama'a ko kuma hallartar duk wasu taruka da ake shirya a kasar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas