1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako wasu 'yan matan Dapchi

Zainab Mohammed Abubakar
March 21, 2018

Gwamnatin Najeriya ta yi alfaharin karbo 'yan matan na sakandaren Dapchi ba tare da biyan wani abu ga mayakan Boko Haram da suka sace 'yan matan. Sai dai masu sharhi kan lamuran tsaro na dasa ayar tambaya.

https://p.dw.com/p/2uhnS
Nigeria Angriff auf Mädchenschule in Dapchi
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Mayakan kungiyar Boko Haram sun maido da yawancin 'yan mata 110 da suka sace a makarantar kwana ta 'yan mata da ke Dapchi jihar Yobe a watan da ya gabata, tare da yin gargadi da kakkausar murya, a cewar wadanda suka ganewa idanunsu.

Rahotanni sun ce da misalin karfe biyu na tsakar dare ne, mayakan suka shiga cikin tsakiyar garin na Dapchin da mayan motoci guda tara dauke da 'yan matan. A daidai lokacin da mazauna garin suka fito cikin firgici, 'yan Boko Haram din sun yi gargadin ga iyaye na kada su sake tura 'ya'yansu mata makaranta.

A ta bakin minisatn yada labaran Najeriya Lai Mohammed, gwamnati bata biya komai kafin sakin 'yan matan ba, sai dai masu sharhi a fannin tsaro na cewa hakan abu ne mai kamar wuya.