An sako malaman Kirista da aka sace a Kamaru
June 1, 2014Ministan harkokin wajen kasar Italiya da kuma fadar Vatikan duk sun sanar da cewa an sako limaman Kirista 'yan kasar Italiya biyu da kuma wata 'yar kasar Kanada wadanda aka sace a kasar Kamaru. Mutanen uku an sace su ne a arewacin kasar ta Kamarun watanni biyu da suka gabata. Shi ma dai ministan sadarwan kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya tabbatar wa manema labarai sakin wadannan turawa biyu wadanda ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka sace su, a kusa da kan iyakar Najeriya da Kamerun. Ministan harkokin wajen Italiya ya mika godiyarsa ga kasar Kanada da Kamaru bisa kokarin da suka yi na sako malaman na addinin Kirista. Amma bai yi wani karin haske ba bisa yadda aka yi mutanen suka kubata.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasir Awal