An sake zaban Abe a matsayin Firaminista | Labarai | DW | 01.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake zaban Abe a matsayin Firaminista

Zaben Firaminista Shinzo Abe ya zo a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ke shirin zuwa Japan inda ake ganin za su maida hankali kan rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa.

A wannan Laraba an sake zaban Shinzo Abe a matsayin Firaministan Japan abin da ke zuwa bayan da jam'iyya mai mulki da kawancenta suka samu rijaye a zaben watan Oktoba, haka zalika abin da ke zuwa kwanaki kafin ziyarar Shugaba Donald Trump na Amirka zuwa kasar, ziyarar da ake sa ran batun takalar Koriya ta Arewa za ta mamayeta.

Abe dan shekaru 63 ya karbi mulki a Disambar 2012 da alkawarin samar da ci gaba a fannin tattalin arziki da bunkasa harkar tsaro, jam'iyyarsa ta 'yan Liberal da kawancensu sun samu kashi biyu bisa uku a zaben da aka yi a ranar 22 ga watan Oktoba, abin da zai bawa firaministan karfin gwiwa a fafutikarsa  ta samar da ci gaba a kasar da samar da sauyi a kundin tsarin mulki. Ana sa ran ya kafa gwamnati da za ta zo da kasafin kudi nan da 31 ga watan Maris 2018, kasafin da zai bada kulawa ta musamman kan yara da bunkasa harkokin masana'antu.