An sake ranar zabe a Kwango
December 20, 2018Talla
Hukumar ta CENI wacce ta sanar da hakan da ranar yau, ta kai zaben ne zuwa ga ranar 30 ga watan nan na Disamba.
Hukumar ta fuskanci matsaloli ne a bangaren samar da takardun zabe, saboda a cewarta konewar da wadanda aka samu suka yi.
Wannan dai shi ne zaben da ake sa ran samun mika mulki daga wata gwamnatin zuwa wata a Kwangon mai fama da rigingimun siyasa. Shekaru biyu ke nan ana tsara zabe ana dagewa a kasar.
Tun da fari dai sai da babbar mai shigar da kara a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Fatou Bensouda, ta yi gargadi kan yiwuwar fuskantar manyan laifuka a zaben kasar Kwangon.