1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kama tsohon shugaban Nissan

April 5, 2019

Wata kotu a Japan ta bayar umurnin ci gaba da tsare tsohon shugaban kamfanin kera motoci na Nissan, Carlos Ghosn, har zuwa ranar 14 ga wannan wata na Afrilu. 

https://p.dw.com/p/3GIf4
Japan Chiyoda Ward Nissan Manager Carlos Ghosn
Hoto: picture-alliance/AP Images/The Yomiuri Shimbun

A jiya Alhamis ne aka mike da Mr. Carlos gidan yarin birnin Tokyo, bayan bayar da belinsa da aka yi a ranar shida ga watan jiya kan zargin aikata almundahana.

Sabon batun da ake kai kan Mr. Carlos, na da alaka ne da zargi kan dala miliyan biyar na wani bangare na kamfanin. Lauyansa ya ce ci gaba da tsare shi rashin adalci ne, kasancewar ya cika dukkanin sharudan samun beli.

Daga cikin kuma zarge-zargen da ke kansa, sun hada har da rashin bayar da bayanai kan yawan albashin da yake dauka, lokacin da yake shugabantar kamfanin. Amma fa Mr.Carlos, ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.