An sake kai hari a Kamaru | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai hari a Kamaru

Rahotannin daga Kamaru na cewar an sake kai wani harin kunar baƙin wake a cikin wani masallaci a kauyen Nguetchewe da ke a yankin arewa mai nisan kan iyaka da Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta ce mutane huɗu suka mutu a nan take a lokacin da wani matashin da ke ɗauke da bam ya kutsa kai a cikin masallacin a lokacin da jama'a ke yin sallah asubahi.

Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Ƙungiyar Boko Haram ke kai irin wannan hari a cikin masallaci a Kamaru.Bayan wanda ta kai a makon jiya a garin Kouyape da ke a arewacin ƙasar wanda a ciki mutane 12 suka rasa rayukansu.