An sake harbe wani lauya har lahira a birnin Bagadaza | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake harbe wani lauya har lahira a birnin Bagadaza

A birnin Bagadaza an bindige wani mai shari´a har lahira, wanda a matsayin sa na lauya, aka shirya zai kare daya daga cikin mutanen da ake tuhuma tare da tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein. Lauyan mai wakiltar tsohon mataimakin shugaba Saddam, shi ne na biyu daga cikin lauyoyin dake kare tsofafin jami´an gwamnatin Iraqi da aka kashe tun bayan fara yi musu shari´a makonni 3 da suka wuce. A kuma halin da ake ciki shugaban Iraqi Jalal Talabani ya na kasar Italiya inda ya gana da FM Silvio Berlusconi. A lokacin ganawar a birnin Rom, shugaba Talabani yayi gargadi game da hanzarta janye dakarun ketare daga kasarsa. Shugaban ya ce janye dakarun gabanin karshen shekara ta 2006 zai kasance wani bala´i ga Iraqi. Italiya dai na da sojoji dubu 3 a kasar, kuma da farko FM Berlusconi ya ce yana iya janye su a cikin wannan shekara.