1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace yara 79 a Kamaru

Abdullahi Tanko Bala
November 5, 2018

Wasu 'yan bindiga sun sace yara yan makaranta su 79 a yankin Bamenda mai magana da harshen Ingilishi a kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/37hoa
Kamerun Bamenda
Hoto: Imago/robertharding

'Yan bindiga wadanda ba a san ko su wanene ba sun sace yara yan makaranta su 79 a yau Litinin a yankin da ake magana da turancin Ingilishi a kasar Kamaru, inda 'yan aware ke gwagwarmayar ballewa domin ayyana 'yancin cin gashin kai a cewar majiyoyin gwamnati da jami'an tsaro.

Garkuwa da mutanen wanda shine mafi muni cikin fiye da shekara guda da ake fama da tashe tashen hankula na zuwa ne yayin da ya rage kwana guda a rantsar da shugaba Paul a wa'adin mulki karo na bakwai.

Wani Jami'in gwamnati yace an sace daliban ne tare da shugaban makarantar da malami daya da kuma direban makarantar.

Wata majiya mai kusaci da makarantar ta tabbatar da sace daliban tare da baiyana cewa galibin daliban da aka sace din maza ne.