An sace wata Bafaransa a birnin Gao na Mali | Labarai | DW | 25.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wata Bafaransa a birnin Gao na Mali

Gwamnatin Faransa ta tabbatar da sace Sophie Petronin da ke aikin agajin kananan yara masu fama da tamowa a yankin Gao na kasar Mali.


Gwamnatin Faransa ta tabbatar da labarin sace wata mata 'yar asalin kasar ta Faransa a birnin Gao na arewacin kasar Mali.  A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi ma'aikatar ministan kula da harakokin kasashen waje ta kasar Faransa ta ce matar wacce aka saci mai suna Sophie Petronin na jagorancin wata kungiya ce mai zaman kanta da ke aikin tallafa wa kananan yara masu fama da cutar tamowa a kasar ta Mali. 

Kakakin fadar Quai d'Orsay ta shugaban kasar Faransar Romain Nadal ya bayyana cewar tuni dai mahukuntan kasar ta Faransa tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Malin suka dauki matakai na ganin an samo wannan mata a cikin gaggawa.

Kawo yanzu dai babu wata Kungiya da ta dauki alhakin sace matar. Sai dai wani gidan radiyo na yankin birnin na Gao ya ruwaito cewar wadanda suka sace matar sun zo ne a cikin wata mota Toyota sanfarin Buzu tsugunne ko kuma Pik-up.