An sace mata dalibai a Bornon Najeriya | Labarai | DW | 15.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace mata dalibai a Bornon Najeriya

Wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yi awan gaba da wasu dalibai mata su 100 daga wata makaranta da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yi awan gaba da wasu dalibai mata su 100 daga wata makaranta a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Sai dai mahukunta sun ce wasu daga cikin matan sun samu sun tsere daga bayan motar da aka kwashe su a ciki, wadda daga kwatancensu, mai kira shigen akori kura ce. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya rawaito kwamishanan 'yan sandan jihar Borno ya na mai cewa an yi gaba da 'yan matan ne daga makarantar Chibok da ke dajin sambisa inda ake zargi nan ne mabuyar 'ya'yan kungiyar.

Masu fafutuka da makaman dai sun harbe soja guda da dan sanda guda wadanda ke tabbatar da tsaro a makarantar kafin su yi awon gaba da 'yan matan 100. Wasu jami'an gwamnatin da suka tabbatar da dawowar kadan daga cikin 'yan mantan da suka tsira, sun ce sun yanka ta dawa ne suka dawo a kafa bayan da wasunsu suka daka tsalle suka dira daga motar. Wasu kuma suka kama rassa bishiyoin dake kasa-kasa suka zamo, yayin da motar mai budaddadar kai ke tafiya.

Da ma dai an rufe makarantun boko a jihar ta Borno amma an maido 'yan matan ne masu shekaru tsakanin 16 da 18 domin rubuta jarabawarsu ta kammala makaranta.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe