An sace ma′aikatan MDD a Sudan | Labarai | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace ma'aikatan MDD a Sudan

Wasu mutane dauke da makamai sun tilasta wa jirgin rarraba abinci na MDD a Sudan saukar dole, kana da yin awun gaba da jami'an da ke cikin jirgin

An kama ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya 'yan kasar Bulgeriya shida, a kasar ta Sudan yayin da suke kan aiki. Mutanen da ake aikin samar da abinci, an tilastawa jirginsu mai saukar angulu sauka, a yankin da gwamnati da 'yan tawaye ke fada da juna. An dai yi imanin cewa 'yan tawayen SPLM su ne suke rike da ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu