An rusa kungiyar ′yan tawayen Seleka | Labarai | DW | 13.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rusa kungiyar 'yan tawayen Seleka

Shugaban rikon kwarya na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Michel Djotodia ya bada sanarwar rusa kungiyar 'yan tawayen nan ta Seleka da ke dauke da makamai a kasar.

Djotodia ya bayyana hakan ne a wannan Juma'ar inda ya kara da cewar daga wannan Juma'a hadakar kungiyar ta 'yan tawaye ta daina aiki a kasar wadda tawaye da jerin juyin mulki ya tagayyara.

Wannan matakin da shugaban ya dauka dai na daga cikin yarjejeniyar da suka kulla da al'ummar kasar a baya na kau da kungiyar da ma sanya 'yan tawayen da ke cikinta su kwance damarsu ta yaki gami da sanyasu cikin rundunar sojin kasar.

Kungiyar ta 'yan tawayen ta Seleka dai wadda Michel Djotodia ke zaman mamba cikinta ita ce ta jagoranci hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize watanni shidda da suka gabata kuma ta share fagen darewa kujerar jagorancin kasar da Djotodia ya yi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal