An rusa gwamnati a Equitorial Guinea
August 11, 2006Talla
Rahotanni daga Equitorial Guinea na nuni dacewa shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo,ya tilastawa prime minista da ministocinsa yin murabus daga mukamansu,wanda zai samar da daman yin garon bawul a gwamnatin wannan kasa dake zama ta 3 a jerin kasashen Afrika masu arzikin man petur.A jiya nedai Shugaba Obiang,wanda ke rike da mulkin Guinea tunda ta samu yancin kai a 1979,a hukuman ya amince da takardun murabus din premier Abia Biteo Borico,da sauran mukarraban gwamnatinsa a wannan kasa dake yammacin Afrika.Shugaba na Guinea dai yasha zargin gwamnatin kasar da rashin inganci musamman a bangaren kula da lafiya da inganta ilimi.Anasaran Shugaba Obiang zai sanar da sabon Prime minista cikin yan kwanaki masu gabatowa.