An rufe zirga-zirgar jiragen sama bayan arangama a filin jirgin saman Tripoli | Labarai | DW | 14.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rufe zirga-zirgar jiragen sama bayan arangama a filin jirgin saman Tripoli

Kasar Libiya na fuskantar tashe-tashen hankulla, inda na baya-bayan nan shi ne arangama tsakanin kungiyoyin mayaka a kewayen filin jirgin saman Tripoli.

Rahotanni daga Tripoli babban birnin kasar Libiya, sun ce arangamar da ta wakana a ranar Lahadi tsakanin bangarorin mayakan kasar a kewayen filin tashi da saukar jiragen sama na Tripoli, ta yi sanadiyar rasuwar mutane shidda, yayin da wasu mutane 25 suka jikkata a cewar ofishin ministan kiwon lafiyar kasar. Tuni dai hukumomin filin jirgin saman suka ba da sanarwar rufe duk wata zirga-zirgar jirage har na tsawon kwanaki uku.

Tsofin 'yan tawayan Zenten ne dai dama suke rike da filin jirgin saman birnin na Tripoli, tare kuma da wasu cibiyoyin soja da ke tsakanin filin jirgin da birnin, tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Muammar Gadhafi. Wasu 'yan bindiga masu kishin Islama suka yi yunkurin kwace wadannan wurare daga hannunsu, abun da yayi sanadiyyar harbe-harbe har ma da manyan makammai, kafin daga bisani masu rike da filin jirgin su yi nasarar korar wadanda suka kai musu harin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal