1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a ci gaba da rufe shafukan intanet din Donald Trump

Abdoulaye Mamane Amadou
January 7, 2021

Kamfanin Facebook zai ci gaba da rufe shafukan Shugaban Amirka Donald Trump na Facebook da Instgram har tsawon makwanni biyun da ke tafe bisa zarginsa da zama barazana.

https://p.dw.com/p/3nekB
USA | Washington DC -  Trumps Königreich
Hoto: imago images/ZUMA Wire/D. Mills

Shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ne ya bayyana haka, yana mai cewar kamfanin ba zai taba barin Shugaba Donald Trump yaci gaba da amfani da shafukansa ba a cikin wannan yanayi mai cike da hatsari da Amirka ta fada, saboda hakan za a ci gaba da toshe kafofin nasa har zuwa wani lokaci.

Tun daga farko dai kamfanin na Facebook ya janye faifan bidiyon da shuga Donald Trump ya wallafa a jiya yana mai kiran magoya bayan sa da su halarci zauren majalisar dokokin kasar, kana daga bisani kamfanin ya toshe kafar tasa har na tsawon sa'o'i 24.