An rufe kasuwanni a Quetta don adawa da harin da ya hallaka lauyoyi | Labarai | DW | 09.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rufe kasuwanni a Quetta don adawa da harin da ya hallaka lauyoyi

'Yan kasuwa da masu sauran hada-hada sun kaurace wa wuraren harkokinsu don adawa da harin kunar bakin wake da ya kashe mutane akalla 70.

A wannan Talata kasuwanni da shaguna da sauran hada-hadar ciniki a birnin Quetta na kasar Pakistan sun kasance a rufe a wani mataki na yin tir da wani harin kunar bakin da aka kai ranar Litinin da ya yi sanadin rayuka akalla 70 daukaci lauyoyi. Hafiz Ullah wani dan kasuwa ne a birnin a Quetta cewa ya yi.

"Kamar yadda kuke gani an rufe kanana da manyan kasuwanni a Quetta, an kuma rufe dukkan hanyoyin da ke shiga kasuwannin. Mummunan abu ne kuma kungiyar 'yan kasuwa ta yi Allah wadai da shi. Muna fata za a tinkari wadannan 'yan ta'adda nan ba da jimawa ba."

Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce kimanin lauyoyi 60 na daga cikin mutanen da aka hallaka a tashin bam din a wani asibitin gwamnati, inda lauyoyin suka hallara don nuna alhini ga kisan gillan da aka yi wa shugaban kungiyar lauyoyin yankin Baluchistan, Bilal Anwar Kasi da sanyin safiyar ranar Litinin.